1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta karbe iko da Rafah da ke iyakar Masar

May 7, 2024

A ci gaba da matsar da Falasdinawa fararen hula daga Rafah zuwa tsakiyar Gaza, gabanin sanarwar Isra'ila na kaddamar da luguden wuta a birnin na Rafah, Isra'ila ta karbe iko da yankin kan iyakar Rafah da ke Masar.

https://p.dw.com/p/4fZX4
Hoto: AFP/Getty Images

Gidan radiyon sojin Isra'ila ne ya sanar da daukar wannan mataki na karbe iko da kan yankin na Rafah da ke kan iyakar Gaza da Masar.

Karin bayani:Amurka ta jaddada adawa da kutsen Isra'ila a Rafah 

Kodayake sojojin Isra'ila sun bayyana cewa nan gaba kadan a wannan rana ta talata zasu fitar da sanarwa kan daukar wannan mataki.

Karin bayani: Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare a zirin Gaza

 Sannan gwamnati Isra'ila ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wutar da ta ce bai kumshi muhimman abubuwan da take bukata ba, duk da cewa a daya bangaren Hamas ta amince da tayin tsagaita bude wuta.