1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya sha alwashin mutunta doka

Abdul-raheem Hassan
May 7, 2024

Masu zanga-zanga da dama sun taru a wajen kotun hukunta man'yan laifuka da ke birnin Hague, suna nuna adawa da matakin rantsar da Shugaba Putin tare da neman kotu ta hukunta shi.

https://p.dw.com/p/4fanc
Shuagban Rasha, Vladimir PutinHoto: Kremlin.ru via REUTERS

Shugaba Vladimir Putin ya sha rantsuwar cigaba da aiki a matsayin shugaban Rasha a karo na biyar, Putin mai shekaru 71 ya  lashe zaben kasar da aka yi a watan Maris da kashi 87 cikin 100, sai dai dai rashin zazzafar adawa daga sauran 'yan takarar ya haddasa ayar tambaya kan ingancin zaben.

Tashohin talabijin na Rasha sun nuna yadda wata motar sulke ta kai Shugaba Putin fadar Kremlin don kaddamar da faretin girmama wa, inda ya lashi takobin kare hakkin 'yan kasar da  kare kundin tsarin mulkinta.

"'Yan kasar Rasha sun yi imani da shugabancinsa kuma sun goyi bayan manufofinsa, ciki har da mamayar Ukraine. Rasha ba ta ki tattaunawa da kasashen Yamma ba, amma Moscow na da nata zabin na muradun kanta."

Shuagba Putin zai kammala sabon wa'adin mulkinsa na shekaru shida a 2030, a lokacin yana da shekaru 77. Masu zanga-zanga da dama sun taru a wajen kotun hukunta man'yan laifuka na Hague don nuna rashin amincewarsu da matakin rantsar da Shugaba Putin tare da neman a hukunta shi.